Ministan ilimi na kasa malam Adamu adamu yayi karin haske dangane da sabon tsarin da suka fitar na bayar da admission zuwa karatu a jami’o’in kasar nan ta hanyar tantancewa tun daga shafin jamb zuwa ga makarantar da dalibi ke nema.

Tun bayan fitar da wannan tsari ne dai jama’a sukayi tofa albarkacin bakinsu inda mafi yawa daga cikin jama’an basu yi na’am da wannan sabon tsari ba domin a ganinsu hakan zai hana “ya “yan talakawa samun damar izinin yin karatu a jami’o’in kasar nan.

Ministan wanda mataimakinshi Mr. Ben. Bem-
Goong ya wakilta a wani taro na manema labarai a yau asabar ya bayyana cewa sabon tsarin bai shafi yadda hukumar kowacce jami’a ke bayar da admission ba, tunda sune dai zasu zabi daliban da suke ganin sun cancanta da su nemi guraben karatu a makarantun nasu..

Yayi bayanin cewa alhakin jamb shine kawai ta tura wa jami’o’in da list din duk daliban da sukaci 180 inda su kuma jami’o’in zasu yi amfani da wadannan sabbin dokokin sai su tantance sannan su mayar da list din zuwa ga hukumar Jamb, wadanda sune zasu sami damar zuwa tantancewa ta gaba a can jami’o’in.

Daga karshe ya bayyan cewar daliban da suka sami nasarar samun admission ta jamb ne kawai zasu biya kudin tantancewar da za’ayi a jami’o’in. Sannan kuma ya gargadi hukomomin jami’o’in da kuma na Jamb akan su tabbatar da cewar sunbi tsarin kamar yadda aka tsara shi…

Tura wa abokanka dake facebook, twitter , whatsapp da sauransu….