Kungiyar masu shirya fina-finai MOPPAN reshen jahar Kano ta bada sanarwar sallamar jarumar yar film din nan Rahama Sadau daga masana’antar film din Hausa ta kannywood.

Wannan mataki dai ya biyo bayan wani video da jarumar ta fito tare da wani mawakin Hausa hip hop inda ta nuna wasu dabi’u da suka saba ma al’adun Hausawa wanda masana’antar ta ginu akai. A bidiyon anga jarumar na rungumar Luka Barnabas(Classiq) wanda hakan ya jawo kakkausar suka ga ita Rahama sadau din.

Sakataren kungiyar Salisu Muhammad shine ya bada wannan sanarwa a wani zama da sukayi da yammacin ranar lahadin nan.

Jarumar dai wacce a yanzu haka tana kasar India bata ce komai ba dangane da wannan mataki da aka dauka akanta.


Photo: Rahama Sadau a India

Ga wadanda suke son suga wannan bidiyo da yayi sanadiyyar korar Rahama daga kannywood sai ku shiga nan gurin