Jama’a barkanku da warhaka, shin ko kuna da masaniya akan wata sabuwar offer ta data da kamfanin MTN suka fiddo da ita wacce ke baka damar samun 1GB akan Naira dari biyar (N500) kacal.

Zaku iya tambaya akan ko ta yaya hakan zai yiwu. Kawai abinda ake bukata shine ya kasance kasa N500 a layinka sai ka koma tsarin MTN iPulse (*406*1#) , amma ka fara komawa kafin ka sanya kudin. Bayan haka, sai kasa *406*2# wanda hakan zai baka damar siyen 500MB.

Kamar yadda kamfanin MTN suka fada cewar duk wanda ya sayi wannan 500MB din to zasu bashi wasu 500MB din, kaga in ka hadasu 1 GB kenan.

Kada ka manta da cewar ita dai wannan data zata yi expire ne a cikin kwana 7 (sati daya.). Har yanzu dai ban gwada ba, amma kamar yadda MTN suka sanar, to da alamun alfanu a ciki.