Mun Ba Yan Arewa Wata Uku Su Bar Yankin Mu – Inji Yan Niger Delta

yan Niger Delta

Gamayyar kungiyar matasa da kuma yan fafutuka na yankin sun fitar da wata sabuwar sanar a jiya alhamis inda suka bukaci duk wani da Arewa mazauni yankinsu da ya tattara kayanshi ya bar musu yanki a cikin wata uku(wato kafin 1 ga watan Oktoba shekarar 2017).

Wannan sanarwar dai ta biyo bayan wa’adin da gamayyar matasan arewa suka ba duka yan kabilar Igbo dake zaune a yankin na cewar su tattara inasu-inasu su bar yankin cikin wata uku tunda sun gaji da zama a Nigeria.

Sun kara da cewar har yanzu babu wani daga cikin matasan arewa da aka kama biyon bayan wa’adin saboda haka yasa suka yanke shawarar korar duk wani dan arewa dake yankin nasu.

Sannan sun kara da cewar duk wani dan arewa da ya mallaki rijiyar mai a yankin nasu sai yayi kokarin kwashe kayansa. Haka zalika sun bukaci a dawo da Ma’aikatar mai ta NNPC zuwa yankinsu sannan kuma a baiwa dan yankinsu shugabancin ma’aikatar.

A cikin makon nan ne dai mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya gana da kingiyoyin manyan kabilun Nigeria dangane da batun, inda daga karshe ya bada sanarwar cewar za’a hukunta duk wanda aka samu da laifin tada zaune tsaye..

Ads