Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa Kannywood kuma ‘yar siyasa wato Rashida Adamu mai sa’a ta bayyana cewa suna matukar shan wahala yanzu wajen samun mazajen aure.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a ‘yan kwanakin nan kamar yadda Mujallar fim ta ruwaito, ta bayyana cewa a duk lokacin da ta samu mijin aure, to fa da gudu zata aure shi.

Jarumar ta kara da cewa: “Samun Mazan Ne Da Wahala, Amma Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Zan Yi Aure”.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jarumar tuni ta dauke kafar ta daga fitowa a matsayin jaruma a cikin fina-finai sannan kuma ta tsunduma cikin harkokin siyasa inda daga baya ma har ta samu mukamin mai bayar da shawara ga Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •