Share this on:
 • 25
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  25
  Shares

Jama’a maziyarta shafin arewamobile.com barkan ku da wannan lokaci na safiyar ranar laraba. Fatan kuna cikin ingantaccen yanayi a yayin karanta wannan rubutu da ni Deendabai nayi akan mutane biyar da suka fi kowa kudi a duniya.

Idan baku manta ba a bara ma munyi wani post mai taken Jerin Mutane Goma Da suka Fi Kowa Kudi A Nigeria a wannan kafa tamu ta arewamobile.com, to yauma cikin ikon Allah gamu da wani post din makamancin wancan.

A farkon watannan da muke ciki ne dai shafin forbes mai wallafa sunaye gami da yawa tarin dukiyar da manya-manyan yan kasuwa na duniya su ka mallaka a shafin nasu ne suka fitar da yawan tsabar kudin wasu daga cikin manyan masu kudin duniya.

A iya sanin mafi yawan masu karatu, shahararren dan kasuwar nan na fasahar zamani Bill Gates shine wanda yake kan gaba a yawan tarin dukiya a duniya. A ranar alhamis, 03 ga watan August da muke ciki aka samu wani attajiri da ya darar ma Bill Gates din a tarin dukiya na wasu yan awanni kafin daga bisani zuwa yammacin ranar Bill Gates din ya koma matsayinsa.

Shahararren dan kasuwar nan alhaji Aliko Dangote ma ya samu damar shiga cikin jerin mutane dari da hamsin (150) na duniya inda ya fado a matsayin mutum na dari da biyar (105) da tarin dukiya da takai dala biliyan goma sha shida da digo biyu($16.2billion) wanda yai daidai da Naira Trillion biyar da digo tara (N5945 T ko kuma N5.945 trillion). Alhaji Aliko Dangote dai na nan har yanzu a matsayin sa na 1 a kudi a Nigeria dama a Africa baki daya.

2

Mike Adenuga shahararren dan kasuwar nan na katafaren kamfanin sadarwar nan na Globacom Nigeria(kamfanin Glo) shine ke takewa Alhaji Aliko Dangote baya a Nigeria da tsabar kudi da suka kai dala biliyan shida da digo biyu ($6.2 billion) wanda suke daidai da naira trillion biyu da digo biyu ( N2.263 trillion) a kudin Nigeria.

Haka zalika shahararriyar yar kasuwar ta nan kuma mace yar kasuwa da tafi kowacce mace kudi a Africa wato Folorunsho Alakija ta kamfanin Famfa Oil ma ta samu damar shiga wannan jeri da tarin dukiya da takai dala biliyan daya da digo shida ( $1.6 billion) wato naira biliyan dari biyar da tamanin da hudu ( N584 billion) a kudin Nigeria.

Bari in yanke surutun iya nan in tsunduma zuwa ainihin labarin da masu karatu suka zo nema a shafin mu mai albarka na arewamobile.com wanda ke kawo muku bayanai akan abubuwan dake waka a bangarori da dama na duniyar nan.

Ga jerin mutane biyar dake kan gaba a kudi a duniya..

5.

Mark Elliot Zuckerberg

Mark Zuckerberg an haifeshi a Newyork ranar Litinin 14 ga watan May a shekara ta 1984 a takaice dai shekarunsa 33. Mark Zuckerberg shine mutum na biyar a cikin jerin masu kudin duniya. Haka zalika shine ake ma kallon mai kudi mafi karancin shekaru.

Mark Zuckerberg shine wanda ya assasa babbar kafar nan ta sadarwa wato Facebook kuma yake a matsayin shugaba mai zartar da tsarukan kafar wato CEO (chief executive officer). Haka zalika shine keda kafar sadarwa ta whatsapp da sauran wasu kaddarori.

Mark Zuckerberg yayi karatun digirinsa a bangaren Computer Science a jami’ar Harvard dake kasar Amurka. Ya fuskanci kalubale biyo bayan fito da kafar sadarwa ta Facebook da yayi a yayin da yake karatu wanda har ta kaiga ya dakatar da kararun nasa a shekarar shi ta karshe a wannan jami’a. A 28 ga watan May na 2017 din da muke ciki ne dai aka kira shi Mark Zuckerberg din aka bashi Certificate na kammala digiri din nasa.

Tarin dukiya: Biliyan ($72.5billion wanda yayi daidai da Naira trillion ashirin da shida da digo 5 N26.5 trillion).

4.

Warren Edward Buffett

An haifi Warren Buffett a 30 ga watan August shekarar ta 1930 wato a yanzu dai yana da shekara 87. Warren Buffett shine mutum na hudu a cikin jerin masu kudin duniya. Warren Buffett shine ke shugabantar kamfanin Berkshire Hathaway Inc sannan kuma ya shahara sosai wajen zuba hannun jari a bangarorin kasuwanci da dama; kama daga bangaren harkar sufuri ta jirage, zuwa kayan kwalliya, zuwa wayoyin sadarwa da sauransu.

Warren Buffett ya fara karatunsa a jami’ar Pennsylvania inda daga bisani yayi taransfa(transfer) zuwa jami’ar Nebraska–Lincoln inda ya karasa digiri din nasa. Buffett ya fadada karatunsa a jami’ar Columbia kafin daga bisani yazo ya tsunduma cikin harkar kasuwanci.

Tarin dukiya : dala biliyan saba’in da hudu da digo biyar (font color=”red”>$74.5) wanda yayi daidai da Naira trillion ashirin da bakwai da digo biyu (N27.2 trillion).

3.

Amancio Ortega Gaona

An haife shi a 28 ga watan March shekara ta 1936 a kasar Spain wato yanzu yana da shekara 81 kenan. Shidai Amancio Ortega shine yake mazaunin na uku a jerin masu kudi na duniya. Ortega babban dan kasuwa ne da ya assasa kamfanin Inditex shahararren kamfanin kayan sawa da suka yi suna sosai da kayan sawa na Zara Clothing.

Amancio Ortega dai ya bar makaranta yana dan shekara 14 saboda yanayin aikin mahaifinsa na ma’ikacin jirgin kasa, inda suka koma wani gari da ake kira Coruña a kasar spain, wanda a nan ne ya kowa yanda ake hada kayan sawa. To a haka dai Ortega bai samu yayi karatu ba har ya afka cikin kasuwanci.

Tarin dukiya : dala biliyan tamanin da biyu da digo bakwai ($82.7 billion) wanda suke daidai da Naira trillion talatin da digo biyu (N30.2 trillion)

2.

Jeff Bezos

An haifeshi a 12 ga watan January shekarar ta 1964. Jeff Bezos ya kasance shahararren dan kasuwane da ya kware sosai wajen yin amfani da fasahar zamani wajen tafiyar da kasuwancin shi. Jeff Bezos shine wanda ya assasa babbar kafar nan ta siye da siyarwa a yanar gizo-gizo wato Amazon wanda kuma yake mazaunin CEO na ita wannan kafa.

Jeff Bezos shine wanda yake mazaunin mutum na biyu a cikin jerin masu kudin duniya wanda a farkon watan August dinnan da muke ciki sai ya kaiga ya hau kan matakin farko na wasu yan awoyi kafin daga bisani ya dawo zuwa mataki na biyun da yake a yanzu.

Jeff Bezos dai yayi karatun digirinsa ne a jami’ar Princeton dake New jersey a kasar Amurka inda ya karbi kwalayen digiri guda biyu wato a Computer Science tare da kuma Electrical Engineering.

Bezos kafin isowarsa jami’ar Princeton ya kasance hazikin dalibi mai kwazo wanda hakan ya bashi damar karbar kyaututtuka da yawa.

Tarin dukiya : dala biliyan tamanin da tara da digo uku ($89.3 billion) wanda yai daidai da Naira trillion talatin da biyu da digo shida (N32.6 trillion).

1.

William Henry Gates III

Shidai William Henry Gates III wanda aka fi sani da Bill Gates an haife shine a birnin Washington dake kasar Amurka a 28 ga watan October a shekara ta 1955. Bill Gates ya kasance a mataki na daya a cikin jerin masu kudin duniya. Shine wanda ya fi kowa bada gudummawa a wajen assasa kamfanin Microsoft Computer wanda hakan ya bashi damar zama babban jigo a kamfanin.

Haka zalika Bill Gates ya kasance shahararren dan kasuwa wajen zuba hannun jari a bangarorin kasuwanci da dama..

Iyayen Bill Gates sun kuduri cewa zai karanci bangaren shari’ane idan ya tashi karatunsa na jami’a. Sai dai kuma sunyi rashin sa’a domin ko shi Bill Gates yafi sha’awar karantar abubuwan da suka shafi programming na kwamfyuta domin ko tun lokacin da aka sanya shi a wata makaranta mai zaman kanta Lakeside School dake a birnin Washington na kasar Amurka ya bayyana hakan.

Bayan kammala Lakeside School Bill Gates ya tafi zuwa jami’ar Harvard inda yake karantar Computer Science amma bayan shekara biyu sai ya aje karatun don mayar da hankalinsa zuwa bangaren rubuta programming(yaren kwamfyuta)

Tarin dukiya : dala biliyan chasa’in da digo bakwai ($90.7 billion) wanda yayi daidai da Naira trillion talatin da uku da digo daya (N33.1 trillion).
Source: http://www.arewamobile.com

Marubucin : Deendabai na shafin arewamobile.com. Ba’a yarda wani ya kwafi wannan rubutu namu ba ba tare da yabar trademark na backlink dake a sama ba wanda zai nuna ainihin asalin rubutun.

Zaku iya turo mana tambayoyinku ta lambar mu ta Whatsapp 08135658217 ko email namu admin@arewamobile.com. Ko kuma ta hanyar yin tambaya ta comment box dake kasa.

Haka zalika ma in kuna da organization dake bukatar ayi mata rubuce-rubuce to kuma zaku iya tuntubar mu.

Deendabai
CEO, arewamobile.com..


Share this on:
 • 25
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  25
  Shares