Kimanin mutane dubu bakwai ne mazauna garin Gomboru Ngala suka koma gidajensu tun bayan farmaki da yan Bokoharam suka sha kaiwa garin a lokutan baya.

Shugaban karamar hukumar Gomborun wato Alhaji Abdulrahman Abdulkarim ne ya bayyana hakan yau asabar dinnan ga manema labarai a birning Maiduguri dake can jihar Borno.

Ya bayyana cewa kwana uku da suka wuce yaje Gomboru domin taimakawa al’umma da kayan abinci da kuma wasu abubuwan na masarufi da zasu fara amfani dasu wajen samun saukin rayuwa..

Daga cikin abubuwan da aka bada sun hada da buhun shinkafa, da man girki ga kowanne magidanci. Dukda dai hakan ya danganta ga yawan iyalan magidancin.

Ya yabawa mazauna garin wajen taimakawa wasu daga cikin mutanen garin da aka konawa gidaje ta wajen basu masaukai a gidajensu domin suma su samu su zauna kafin su gyara nasu. Sannan kuma ya bukaci al’ummar garin dasu hada kansu wajen tunkarar duk wani abu da suka ga yana yunkurin cutar dasu..

Idan dai za’a iya tunawa, yan Bokoharam sun kaiwa garin Gomboru Hari kimanin shekara biyu da suka wuce inda suka kashe mutane da yawa tare da tilastawa wajen mutum dubu hamsin barin garin..