Sanata Kabiru Marafa na Jam’iyyar APC da ke Wakiltar Jihar Zamfara a Majalisar Dattawa yayi da’awar kera mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote dukiya inda yace shi na shi mizanin awon dabam.

kabir-marafa data-recalc-dims=

Babban Dan Majalisar yace a wajen sa shi wadatar zuciya ita ce arziki amma ba tsabar kudi ba. Sanatan yace idan kuma wannan ake magana to shi hamshakin attajiri ne don kuwa yana da wadatar zuci kwarai.

Sanatan yace har yanzu hayan gida yake yi a Abuja kuma yace kashi 60% cikin 100% na abin da ya samu hannun mutanen da su ka zabe sa yake komawa. Snatan dai ya nuna cewa bai da handama ko kadan.

Written by Muhammad Malumfashi . Via Naij Hausa

Ads