A yaune shahararren mawakin nan kuma jarumi a harkar film din wasan Hausa na kannywood Adam a zango ya sha alwashin dakatar da yin wasan Hausa tare da yanke shawarar komawa fannin wakoki inda yake ganin zaifi samun saukin aiwatar da harkoki.

Jarumin yayi wannan jawabi ta shafinsa na instagram inda ya kara da baiwa jama’a hakuri dangane da kalaman nasa.

“Salamu Alaikum Warahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. Ni Adam A. Zango zanyi amfani da wannan damar don baiwa masoya kallon fina finaina, producers, directors, actors, and the entire crew of kannywood. hakuri akan na dakatar da yin film. zan tsaya iya waka don in sami sauki da kwanciyar hankali.”

“kuma ina baiwa yan boko hakuri akan abinda @bbchausa sukace na fada game da masu degree agafarceni. GOD BLESS ISLAM,GOD BLESS NIGERIA, GOD BLESS KANNYWOOD.
THANK YOU”

Sai dai jarumin ya nuna rashin jin dadin shi dangane yadda kafafen yada labarai suka yi ta yayata wadancan kalaman nashi wanda har hakan ya jawo fushin wasu daga cikin masoyanshi.

Masoyanshi da dama sun nuna rashin jin dadinsu dangane da wannan matakin da shi jarumin ya dauka, wanda hakan ke nuni da cewar akwai yiwuwar ya janye wannan mataki da ya dauka.

Tura wa abokai..