hoto n abida Muhammad kannywood

Tsohuwar fitacciyar jarumar wasan kwaikwayon Hausa Abida Muhammad ta bayyana cewar a yanzu ta koma bangaren rubuce-rubuce sabanin yadda wasu ke ganin kamar ko cewa ta dawo harkar film din Hausa duba da yadda suke ganinta a masana’antar.

Jarumar ta bayyana hakan ne a hirar ta da mawallafi a shafin labaran yan wasan Hausa na kannywood wato Kannywood Today a wajen taron ranar marubuta ta duniya da ta gudana a Kano , wanda yayi mata wasu yan tambayoyi da zasu zo muku a nan gaba.

Tun bayan rasuwar mijinta, Abida Muhammad bata sake yin wani auren ba, wanda bayan haka ne kuma aka rinka ganinta a cikin yan wasan Hausa wanda hakan yasa wasu suka rika tunanin ko ta dawo harkar film din ne. Ga dai yadda hirar su ta kaya.

Kannywoodtoday: Bari mu fara da yin ta’aziyyar rasuwar maigidanki wanda Allah ya yiwa rasuwa

Abida Muhammad: Alhamdulillahi na gode kwarai bisa wannan ta’aziyya da kuka yi min, Allah yabar zumunci.

Kannywoodtoday: Malama Abida yanzu haka ana ganinki tare da ‘yan fim, shin ko zaki koma cikin sana’ar fina-finan ne?

Abida Muhammad: Game da ganina da ake da abokan harkar fim ba komai ne ya jawo ba illa mutunci da aka saba, mu yanzu a harkar fim ai iyaye ne, sai dai mu bada shawara ga kannenmu don suma su samu abinda zasu samu.

Kannywoodtoday: Ya kike kallon sana’ar fim daga lokacin da kuka bari zuwa yanzu?

Abida Muhammad: Alhamdulillahi an samu cigaba sosai gaskiya, ana ta samun ci gaba kwarai da gaske, sai dai dan abinda ba’a rasa ba kuma cikin ikon Allah komai na warwarewa yadda ya kamata.

photo n abida muhammed Hausa film

Kannywoodtoday: Tunda kince ba fim zaki koma ba wane fanni zaki mayar da hankali?

Abida Muhammad: Insha Allah yanzu na mayar da hankali wajen rubuce rubuce wanda yanzu haka ana kan hakan.

Kannywoodtoday: Shin kin fara rubuta littafi ne?

Abida Muhammad: Kwarai kuwa ina da littatafai guda biyu dake kan hanyar fitowa akwai muguwar kawa da Kuskure na.

Kannywood Today