Fitaccen jarumin wasan kwaikwayon Hausa na Kannywood Adamu Abdullahi wato Adam A Zango ya bayyana cewa daukakar da ya samu ta janyo masa aikata kura-kurai da dama a can baya.


Adam A Zango

Jarumin ya bayyana hakan ne a shafinsa na sadarwar zamani na Instagram, inda ya bayyana nadamar shi na kura-kuren da yayi a can baya gami da shan alwashin gyara wa tunda lokaci bai kure masa ba.

“Nayi kura-kurai da yawa a sanadiyyar daukaka. Sai dai lokaci bai kure min ba. Gyara ya zama dole, Allah ya bamu sa’a. ”

Idan baku manta ba akwai lokacin da jarumin yayi wani furuci da bai yima jama’a da yawa dadi ba. Inda yayi habaici gami da caccakar masu degree wanda hakan har jawo martani mai zafi ta dalilin da har jarumin yayi yunkurin daina harkar film gaba daya a wannan lokacin.

Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu bisa wannan nadama da jarumin yayi inda suka yaba masa kan fahimtar su da yayi.

Ads