Share this on:
 • 78
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  78
  Shares

Fatima Abubakar wacce akafi sani da Fati Shu’uma ta karyata labarin da ake yadawa a kafar Internet cewa tace zata iya fitowa a kowane film.
Ta karyata hakan ne a wani sakon Video ta yada a shafin ta na Instagram.

Tayi bayani cewa ita batayi hira da kowace Jarida ba. Sannan ta kara da cewa ita bata ce tana son Shugaban kasa Muhammadu Buhari da aure ba.

Jarumar daga bisani ta roki jama’a dasu guji yada duk wata jita-jita.

A karshen makon daya gabata ne dai muka tsinci wasu labarai har guda biyu dangane da jarumar, wato kan cewar tace zata iya fitowa a kowanne irin film ne da kuma labarin cewa wai tace tana da burin ta auri shugaba Muhammadu Buhari, labaran da jarumar ta karyata gami da nisanta kanta da su.


Share this on:
 • 78
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  78
  Shares