Share this on:
 • 63
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  63
  Shares

Tun ba yau ba ake rade-radi kan mutuwar auren ta wanda ya sanya har ta kwaso kayanta daga Kano zuwa Kaduna, garin iyayenta.Auren ta na biyu da tsohon mijinta wanda yayi sanadiyar komawar ta Kano, Allah ya albarkace su da yara biyu,Ahmed da Yasmin.

A hirar ta da wakilin jaridar Leadership Ayau, Fati KK ta fayyace masa labarin dalla-dalla kan yadda al’amura suka kasance har suka rabu da mijinta.

Photo: Fimhausa blog

“To ni dai abin da zan iya cewa, ni dai har ga Allah ya sani, wadanda muke tare da su su ma sun sani, na so zaman aure.In da ba na son zama da shi, wallahi ba zan mike kafafu na yi ta zuba ‘ya’ya ba. Na fuskanci gori daban-daban duk na shanye, kuma hakan bai sa ni bijirewa ba har na ce a sake ni ba, na kan zauna in yi kuka, watarana sai na fada masa, sai na gane in har wani ya ki ka, ai Allah na son ka. Na fuskanci kalubale kala-kala, sai dai in ce mun gode Allah.”

Jarumar wacce aka daina jin duriyarta a fagen shirya fim bayan auren ta ta bayyana cewa dangin mijinta sun zargi ta da bijire ma mijinta bayan ta samu labarin cewa zai kara aure. Tace basu fahimce ta ba domin bata da kishin samun kishiya. Haka zalika bazata zabi rabuwa da mijinta kan matsalar rashin kudi/talauci.

“Mun haihu da shi yara biyu, Abu ya ki ci, ya ki cinyewa, a gaskiya talauci bai taba sa na ce zan rabu da wanda nake tare da shi ba. Na dai samu surutai a cikin danginsa, wai don zai kara aure ne na bijire masa na ce ya sake ni, alhalin wallahi tallahi, wallahi tallahi, wallahi tallahi ban san wannan zancen ba, ban ma taba jin sa ba. ”

“Ni na isa na ce ba na son a kawo min kishiya, bayan ni ma na sami wata? Ya kamata a duba wannan maganar kin fahimce ni.
Don shi yana ganin in ya bata ni a idon mutane, shi kuma za a ga farin sa. Don na taba aure na fito yanzun ma na fita gidansa, kuma duk wanda ya duba aure na na farko ya san na ci wuya, wadanda suka je suka gani da wadanda suka ji labari kowa ya Shaida, to wa zan zauna in ba labari har in ce ga matsala ta.”

Jarumar ta gama zaman idda sai dai kuma ta bayyana cewa ita da aure sai an dan kwana biyu domin ita yanzu tsoron maza take.

“To ni dai yanzun ya sake ni, kuma har na ma gama idda na, batun aure kuma ban ce ba zan kara yi ba, amma gaskiya ba yanzu ba. Saboda ni yanzu mazan ma tsoron su nake ji wallahi, nan ka yi aure ka haihu, can ka yi ka haihu, to ina dadin sa.”

“Ni yanzu addu’a ta, Allah Ya kawo wanda in ya aure ni zai rike ni har iya tsawon rayuwata, da ni da ‘ya’yana, tamkar shi ya haife su. Kuma ni ba zan taba zagin shi ko aiban ta shi ba, saboda uban ‘ya’yana ne, ba zan yi abin da yake yi ba, na duk inda ya zauna sai ya yi ta zagi na, har kanwata ya samu ya ce mata in Allah ya yarda sai na wulakanta, abin da ya manta babu wanda aka halicce shi da arziki a Duniya. Karshe dai ina masa fatan alheri” Ta kara.

Yanzu haka Jarumar tana da yara uku, daya daga mijin ta na farko sa’anan biyu daga mijinta na biyu.


Share this on:
 • 63
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  63
  Shares