Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Click to refresh the page before proceeding

Fitaccen jarumin film din Hausa Nura Hussaini da yayi bidiyo na raddi ga Dr. Ahmad Gumi don Kare Baba Buhari ya turo mahaifinsa tare da aminin mahaifinsa, Alhaji Tasi’u Masallacin Sultan Bello Kaduna, domin su ba Sheikh Dr. Ahmad Gumi hakuri kuma su nemar masa gafara.

Idan baku manta ba a kwanankin bayane shahararre kuma fitaccen malamin yayi wani jawabi wanda cikin jawabin ya la’anci duk wanda ya kara zabar gwamnati mai ci a yanzu bisa hujjarshi ta cewar yin hakan na nufin mutum ya yadda a kara komawa cikin wahala.

Wannan magana ta Dr. Ahmad bata yiwa jama’a da yawa dadi ba musamman ma dai magoya bayan shugaba Buhari inda malamin ya samu raddi daga bangaren mutane daban-daban ciki harda wannan jarumi na film wato Nura Hussaini.

Nura Hussaini dai yace shedan ne ya ja shi yin hakan, inda shi kuma Malam Ahmad din yace ya yafe masa kamar yadda muka samu labarin a majiyarmu ta Sarauniya jarida.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •