Share this on:
 • 17
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  17
  Shares

Fasihin hazikin mawakin Hausa mai baiwar hikimar sarrafa harshen Hausa Nura Musa Inuwa wanda aka fi sani da Nura M Inuwa ya bawa masoyan shi da suke ta dakon isowar albums din shi guda biyu masu fitowa a shekarar nan hakuri bisa rashin isowarsu gare su.

sababbin wakokin nura m inuwa wasika 2018

Wadannan kundin wakoki da jama’a ke ta dako sune kundin Wasika da kuma Manyan mata wadanda aka kyautata zaton fitowar su kasuwa a ranar litinin da ta gabata, wato 15th January, 2018 amma sai basu sami fitowa ba saboda da wasu dalilan da masu sauraro basu sani ba.

Mutane da dama sun kagu sosai da su saurari wakokin da ke cikin wadannan kundaye na fasihin mawaki M Inuwa, inda har wasu suka yi ikrarin yin zanga-zanga in ba’a fito da su da wuri ba.

A nashi bangaren, Nura M Inuwa yana ta kokarin kwantar ma da masoyan shi hankali ta hanyar basu hakuri da kuma musu albishir din cewa wadannan kundaye na nan isowa nan ba da jimawa ba, illa iyaka akwai wasu yan gyare-gyare da suke kara yi…

To muma dai anan arewamobile muna nan muna dakon isowar wadannan kundaye na nura m inuwa wato kundin wasika da kuma na manyan mata.


Share this on:
 • 17
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  17
  Shares