Shahararren fasihin mawakin Hausa na kannywood wato Nura Musa Inuwa da aka fi kira da Nura M Inuwa zai yi aure a karshen wannan wata na Aprilu da muke ciki.

Mawakin zai angwance tare da amaryarsa Amina Tijjani Wada wanda za’a daura shi a ranar ashirin da tara ga wannan wata da muke ciki (29th April 2017) a Gangarawa dake garin Malumfashi a Jahar Katsina da misalin karfe biyu na rana(02:00pm) kamar yadda katin gayyata ya bayyanar.

Dama dai jama’a da dama musamman ma masoyan shi wannan fasihin mawakin na ganin cewa ya kamata ace tuntuni mawakin yayi aure, to a yau da alamu dai burinsu ya cika.

Auren Nura M Inuwa

ran yaushe ne daurin auren nura m inuwa

yaushe m inuwa zaiyi aure

Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a mai albarka…