Fitacciyar jarumar Fim din nan da aka
sallama daga Kannywood, Rahama Sadau
ta kafa tarihi, inda tashin farko, Fim dinta
yayi suna tare da karbuwa a masana’antar
Kannywood.

Mun samu labari cewa Fim din na Rariya ya kayatar da yan kallo sosai dasosai, har ma ya tsere ma manyan Finai finai da aka fitar a wanann shekara kamar su ‘Yar Fim’, ‘Mansoor’, Dan kuka’ da Zinaru.

fim din na rariya ankalleshi ne a watan Yunin bana, inda aka kalle shi a garuruwan Abuja da Kano, hakan yasa yan kallo suka dinga shaukin fitarsa gaba daya.

Shi dai Fim din Rariya ya kunshi jarumai kamar su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Hafsat Idris, Fati Washa, Maryam Booth da sauransu, sa’annnan Yaseen Auwal ne ya bada umarnin.

An shirya Fim din ne da nufin fadakar da al’umma kan sauyin da zamani ya kawo, musamman a jami’o’i, ta irin kayan da ake sawa, da kuma rayuwar karya da wasu daliban ke yi.