Share this on:
 • 15
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  15
  Shares

arewamobile ta zakulo muku jerin sababbin fina-finan Hausa masu fitowa a shekarar bana ta 2019. Kannywood kan fitar da fina-finai da dama duk shekara. Ga jerin fina-finai masu fitowa bana.

1. SAREENA

Bayan film din MANSOOR da MUJADALA wanda shahararrun masu shirya film Sarki Ali Nuhu da kuma Abubakar Bashir Mai Shadda suka kawo muku, yau ma gasu dauke da wani kayataccen film mai suna SAREENA wanda aka fara daukar shi satin da ya gabata kuma ake cigaba da daukar shi a yanzu haka.

Daga cikin yan wasan dake haskawa a wannan sabon film akwai Umar m sharif, Maryam Yahaya, Ali nuhu, Abba El Mustapha da dai sauransu.

2. HAFEEZ

Shima film din Hafeez sabon fim ne da Abubakar Bashir Mai Shadda, UUGP ya shirya wanda fitaccen jarumin kannywood, Ali Nuhu ya bada umarni.

Yan wasan da suka haska a wannan film sun hada da Umar m shareef, Maryam Yahaya, Ali nuhu, Abba El-Mustapha, Bilkisu Shema, Yakubu Muhammad, Aishat Humaira, Salisu S Fulani da dai sauransu.

Wadanda suka rera waka a fim din Hafeez sune:
Abdul D One
Hamisu Breaker
Nura M Inuwa
Umar M Sharif

Za’a fara haska film din ranar murnar haihuwar sarki Ali Nuhu wato ranar 15 ga watan Maris(March) a film house cinema dake Ado Bayero Mall, Shoprite Kano.

3. SADAUKI

Sadauki sabon film ne daga shahararren mai shiryawa kuma mai bada umarni wato Hassan Giggs wanda ya shirya kuma ya bada umarnin shirin wanda za’a haska shi a cikin garin Zaria a ranar 25,26 da kuma 27 ga watan Janairu nan da muke ciki.

Jaruman film din Sadauki sun hada da Adam A Zango, Fati Washa, Fateema makamashi, Tijjani Asase, Alhassan Kwalle da sauransu.

Daga cikin karin sabbin fina finan Hausa da zasu fito a bana akwai film din Zan Rayu Dake wanda sarki Ali Nuhu ya gabatar, Manyan Gobe daga Mai Shadda investment, Wutar Kara shima daga Mai Shadda Investment, Ana Dara, Sarauniya, Ramuwar Gayya, dadai sauran su.


Share this on:
 • 15
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  15
  Shares