Wadannan sune sababbin wakokin fasihin mawaki Nura M Inuwa na shekarar bana ta 2018 wadanda ya saki a cikin albums dinsa guda biyu wato wasika da kuma manyan mata.

Kamar dai yadda fasihin mawakin ya saba fito muko da wakoki daga shekara zuwa shekara, wannan lokaci ma hakan akayi inda ya fito muku da kundin wakokinsa har guda biyu.

Album din wasika na Nura M Inuwa dai na dauke da wakoki guda goma sha shida (16) a yayin da dayan kundin nasa wato na Manyan Mata ke dauke da wakoki goma sha biyar (15) wadanda zamu baku links da zaku sauke su zuwa na’urorin ku.

Album din Wasika ya kunshi wakoki kamar haka : Wasika, Ruwan Ido Duniyar Masoya, Matar Mijina, Dan Gwamna, Gimbiya, Kaunar Ki Nake, Labarina, Masoyan Wake Na, Matan Zamani, Mun Shaku Da Juna, Na Tafi Na Dawo, Na Zabe Ki, Inda Rai Da Rabo, da kuma Madubin Dubawa.

Sauke wakokin album din Wasika daga shafin arewablog ta hanyar latsa wannan link din .

Album din Manyan Mata na dauke da wakoki kamar haka : Ana Dara Ga Dare, Best Of Manyan Mata, Aure Na Soyayya, Mata, Ba Cinikina Bane, Buga Tambura, Halimatu Sadiya, Aisha Happy Birthday, Wata Ruga, American University Candy, Ummina, Uwar Amarya, Yaran Mata, Roman Baka, da kuma tallar sabon album dinsa na shekarar badi (2019) in Allah ya kaimu wato album din Mai Zamani 2019.

Haka nan ma zaku iya samun wakokin album din Manyan Mata duka daga shafin arewablog ta wannan link din