Share this on:
 • 43
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  43
  Shares

Fasihin mawakin nan Nura Musa wanda aka fi sani da Nura M Inuwa ya saki sababbin albums na wakokin shi na shekarar bana ta 2018 masu taken Wasika da kuma Manyan Mata.

Tun farkon shigowar wannan sabuwar shekarar ne masoyan wannan hazikin mawaki suka yi ta jiran tsammanin fitowar album din wakokin nasa wanda a yau ya share musu hawaye ya sako musu su ya zuwa kasuwa.

Shiga nan gurin domin sauke duka wakokin album din Wasika dana album din Manyan Mata

A yanzu haka zaku iya samun wadannan wakoki dake cikin albums din a shagunan da ake ciniki da dillancin fina-finai da wakokin Hausa na Kannywood musamman wadanda ke Kano, Kaduna, Katsina da sauransu.

Daga yanayin rubututtuka da hotuna da hazikin mawakin ya dora a shafinsa na sadarwar zamani na Instagram ya nuna cewa jama’a sun yi maraba da wakokin nasa inda yanzu haka suke ta rububin siya.

Ga wasu daga cikin hotunan da muka ciro a shafinsa na Instagram


Share this on:
 • 43
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  43
  Shares