Fitaccen mai hada gami da bada umarni a harkar wasan kwaikwayon na Hausa kannywood wato Falalu Dorayi yayi tsokaci kan sabon tsarin da zasu zo dashi wajen fitarda sababbin fina-finai masu zuwa a nan gaba.

Yayi wannan tsokaci ne dai a wani hoton bidiyon youtube inda ya bayyana cewar tsarin yadda zasu rika fitar da film a yanzu zai sha ban-bam da yadda aka rinka fitar dashi a can baya.

Daga yanzu duk film din da zai fito sai an kalle shi a gidajen Cinema, gidajen gala, manya-manyan gidajen kallo kafin a shigo dashi ya zuwa hannun yan kasuwa masu dillancin fina-finan.

Haka zalika ya kara da cewar zasu zauna da masu downloading a kwamfyuta tare da kungiyar tace fina-finai don fitar da wani tsari da zai kasance anyi wa kowa adalci a harkar.

Daga karshe ya bayyana cewar daga yanzu duk wani film da zai fito to zasu sanar da ranar da za’a kalle shi a gidajen Cinema da sauran gidajen kallo gabanin a sake shi zuwa kasuwa.