Share this on:
 • 37
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  37
  Shares

Muna ma jama’a masu bibiyar wannan shafi namu mai albarka wato arewamobile.com lale a wannan lokaci. Kamar kullum, Deendabai ne ke tare da ku a wannan lokaci inda zanyi muku dan takaitaccen bayani kan wata manhaja(app) ta android mai amfani sosai musamman ta bangaren tsaron kan wayar(phone security).

Wayar android dai ta kasance wayar da aka fi amfani da ita a wannan zamani da muke ciki musamman ma a wannan yanki namu na nahiyar Africa, a takaice dai a kasa ta Nigeria. Wayar ta samu karbuwa ne bisa irin ayyuka masu muhimmanci da al’umma kan yi da ita ta kusan ko wanne bangare na rayuwa.

Daga cikin muhimman abubuwa da akanyi da waya kirar android akwai ajiye wasu bayanai, hotuna, bidiyoyi, litattafai, bayanan sirri da sauran wasu fayiloli masu matukar amfani ga mutum.

Duba da irin karbuwar da wayar android ta samu gami kuma da irin abubuwan da jama’a kanyi da ita masu muhimmanci yasa masu amfani da ita yin amfani da tsarin tsaro na PIN, Password, Pattern, Voice recognition ya zuwa aiki da wasu manhajoji(apps) na tsaro da dai sauran makamantansu don kare wasu bayanai nasu masu muhimmancin da baza su so wani ya kasance ya gani ba.

Duk da irin wannan tsaro da akan sanya, wasu sukan yi yinkurin bude wayarka ta hanyar cankar lambobin tsaron da ka kulle wayar taka wanda hakan ka iya haddasa matsala biyo bayan sanya lambobin da yawa ba daidai ba.

Domin sanya wayarka ta dauki hoton koma waye yayi kokarin bude ta zamu bukaci yin amfani da manhajar android me suna Hidden Eye wanda zaku iya samu a playstore a kyauta.

Bayan ka dakko wannan manhaja zuwa wayarka kawai sai ka bude ta domin aiwatar dai saituka akanta.

Da farko zaka ga wani guri da aka rubuta Security status sai ka maida shi ON daga nan sai ka sauka kasa inda zaka ga wasu akwatuna dauke da wasu rubutuka kamar haka:

hidden eye

Sai ka zabi show intruders on unlock , amma zaka iya zabar sauran zabukan.

Shikenan wayarka zata rika daukar hoton duk wanda ya dauki wayarka yayi kokarin cire password ko pattern dake kanta.

Akwai wasu manhajojin daban da zaka iya amfani da su kamar irinsu LockWatch- Thief Catcher da sauran makamantansu.


Share this on:
 • 37
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  37
  Shares