Jarumar Kannywood Rabi Ismail

An sake kama jarumar wasan Hausa Rabi Ismail bayan guduwa da tayi daga gidan yari shekara shida da suka wuce da yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya da wata babbar kotu a Kano tayi.

An tuhumi jarumar ne dai da laifin kisan saurayinta mai suna Auwal Ibrahim ta hanyar tunkudashi cikin dam din Tiga bayanda ta shayar dashi kwayoyi masu sa maye a cikin cakuleti(chocolate) .

Bayan yanke mata hukuncin kisan ne da akayi a December 2011 sai aka tasa keyarta ta zuwa gidan kaso dake Kaduna, inda daga bisani kuma aka mayar da ita gidan yarin Hadejia jahar Jigawa wanda daga can ne ta samu hanyar kubucewa.

Hadin gwuiwar rundar yan sanda farin kaya(sss) da kuma na yan sanda ne suka sami nasarar cafko jarumar.

Ads