Fitaccen jarumin film din hausa kuma mai kamfanin FKD wato Sarki Ali Nuhu ya bayyan lokacin da zai saki film din mansoor a shafinsa na twitter.

Jarumin ya baayyana lokacin ne biyo bayan wata tambaya da wani mai masa fatan alkairi yayi cewa ” Allah yataimaki Sarki yaushe zaku sakar mana film din mansoor ne??”

Sarki Ali yabashi amsa da cewa ” Karshen wannan watan Insha Allah”

Da wannan ne muke sa ran fitar wannan kayatatten wasan kwaikwayo karshen wannan wata na satunba. Shidai film din mansoor ya kunshi wani labari ne nawani matashi da soyayya tasashi nemo asalinshi.