Jama’a barkanmu da warhaka , ina muku marhabun da zuwa shafin arewamobile.

download-google-duo-android

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya nayi wani rubutu akan Google allo, sabon application da ake sa ran zaifi whatsapp dadi . A yau muna dauki da darasi akan sabon application na kira ido da ido wato video calling wanda kamfanin google suka kirkira kuma suka sake shi a farkon watannan na September.

Google Duo zai kasance ya maye gurbin skype a wayoyin hannu sabili da saukin aikinshi gami da kuma rashin ka’idoji masu yawa.
Wasu daga cikin abubuwan dake tattare da google duo

• Video calling kai tsaye akan kowacce irin wayar android ko iPhone zuwa kowacce muddun duka suna da app din akansu, ma’ana baya bukatar yanayin version na waya.

Knock knock : zai baka damar ganin yadda mutum yake gabanin ka dauki wayarsa.

• Yana fidda hoton video mai kyawun gaske ( HD videos ) sannan kuma yana aiki akan irin network (2G ko 3G)

* Domin fara amfani da wannan application din kawai sai ka shiga playstore ko iTunes ka dauko shi wannan app din zuwa wayarka. Daga nan kuma sai kayi register ta amfani da lambar wayarka domin itace abinda aka fi bukata a wannan application.

– Ga masu amfani da wayoyin android sai ku shiga wannan link din da ke kasa domin sauko dashi zuwa kan wayoyinku:
Download google duo onto your android phone ko kuma kayi search dinsa a playstore.

– Masu amfani da apple iPhone suma zasu iya sauko dashi daga wannan link dake kasa:
Download google duo for iPhone ko kuma ka nemeshi a iTunes.

Samari da yan mata wannan app naku ne don kara jin dadin soyayya sakamakon ganin juna da zaku rika yi yayin da kuke soyewa. Haka zalika wannan app zai kasance mai matukar amfani ga wadanda suka dade da barin gida musamman dalibai da sauran makamantan su. Tammat bihamdillah!

Ku tura wannan post zuwa ga abokanenku dake kafafen Facebook , Whatsapp , Twitter da sauransu.