Jama’a barkanku da wannan lokaci na yammacin ranar laraba. A makon da ya gabata ne dai muka kawo muku labarin ce mawaki Nura M Inuwa Zai Yi Aure A Karshen Watannan
na Aprilu, wato ranar Asabar 29-April-2017 wanda za’a daura a garin Malumfashi dake jahar Katsina.

Sababbin Wakokin Auren Nura M Inuwa

Kasantuwar sa na fasihin mawaki da ya kware sosai ta bangaren wakokin soyayya zuwa ga wakokin da suka shafi rayuwar yau da kullum, yasa shima wasu mawakan su
ka yanke shawarar yi masa kara wajen wake shi tare da amaryar tashi Amina.

Bisa ga tsari da dokar kare hakkin malaka ta tanadar, baza mu samu damar cigaba da dora muku sababbin wakokin fasihan mawakin Hausa Nura M Inuwa ba, sai dai zaku iya samun bayanai akan lokaci da kuma guraren da zaku iya samun wakokin su a shagunan kasuwanni dana yanar gizo-gizo.

Domin samun sababbin wakokin albums na nura m inuwa sai ku rinka bibiyar shi a shafinsa na sadarwar zamani na Instagram ko ta Facebook ko kuma ku duba iTunes.

Duk da haka zaku iya cigaba da Kasancewa da mu a arewamobile.com don samun bayanan kan lokaci da kuma gurare da zaku iya samun sababbin wakokin nura m inuwa.

Ads