Ado Gwanja kwankwasawa Kwankwasiyya Song 2017

Wannan wata sabuwar waka ce da shahararren mawakin nan wato Ado Isa Gwanja yayi mai girma Engineer Dr. Rabiu Musa kwankwaso dangane da abubuwan dake faruwa tsakaninshi gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Idan baku mance ba a yan kwanakin baya ne aka kama shahararren mawakin nan wato Sadik zazzabi bisa wakar da yayi wa kwankwaso inda a cikin Wakar ya kasance yayi habai ci wa gwamna ganduje. Daga bisani kuma Dauda Adamu Abdullahi Kahutu wato Dauda Rarara yazo da tashi sabuwar wakar dauke da yabo ga gwamna Ganduje tare da suka ga Dr. Rabiu Kwankwaso wanda hakan ya jawo har aka kona masa gida da wasu abubuwan nasa.

A yau kuma ga Ado Isa Gwanja da tashi sabuwar wakar ta nuna goyon baya ga Sanata Rabiu Musa kwankwaso, inda a cikin wakar yake bayyana cewa goge sunan kwankwaso da aka yi a Kwankwasiyya da amana city bazai sanya a mance da shi ba.

#Baitoci

Kwankwasawa kowa yaje ya shirya ya fito biyu da sha tara mun tunkuda mukai har bango..

Dr. Rabiu Musa ba kamar ka, babu mai fasa tushenka Kwankwasiyya.

Tafi gaba kafi na baya ba kamar ka, babu mai rufe shafinka Kwankwasiyya.

Sauko Da Wakar Ado Gwanja Kwankwasiyya 2017