A makon da ya gabata ne shahararren mawakin nan na Hausa hip hop wato Buba Barnabas Luka wanda aka fi sani da Classiq ya fidda wata sabuwar waka ta video da ya yiwa lakabi da “I love you ft avala” wanda sukayi tare da fitacciyar yar wasan Hausa ta kannywood Rahama sadau.

Classiq dai dan asalin jihar Bauchi ne, amma galibin rayuwarsa yayita ne a Kano ta dabu inda ya samu yin degree dinsa a fannin ilimin kwamfyuta mai kwakwalwa a jami’ar Bayero ( BUK) dake kano.

Classiq ya fara waqa ne tun yana kimanin dan shekara sha shida, inda bayyan kammala karatunsa ne ya tsunduma cikin harkar gadan-gadan.

Classiq dai a can baya yasha yin waka da wasu manya mawaka daga kudancin Nigeria irinsu Wande Coal, Davido , Eldee , Uzi, Phyno, Reminisce da sauransu.

A baya bayan nan ne ya fitar da sabuwar wakarshi ta bidiyo wacce yayi da rahama sadau wanda hakan ya jawo maganganu da yawa ganin yadda ita Rahamar ta nuna wasu dabi’u da ba’a san yayan Hausawa da nuna irinsu ba.


Photo: PremiumTimesNg

Sauko da wannan video daga shafin abokina, pressloaded.com sannan sai ka dawo arewamobile ka bayyana mana ra’ayinka dangane da wannan video…

Download it here

#Rahama_sadau_Classiq
#Classic_Rahama-Sadau_Video
#Video_Rahama-Classiq