Share this on:
 • 33
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  33
  Shares

Birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa na ta kara kokarin ganin ya cigaba da zama birni mafi kyawu da wayewa a zamance inda ako da yaushe mahukuntan birnin ke kokarin ganin sun kawo abinda zai kayata gami da inganta rayuwar al’ummar dake zaune a birnin.

A cikin makon nan ne dai hukumar yansandan birnin ta fara horar da jami’anta kan amfani da wani sabon babur me tashi sama da zasu rika aiki dashi a cikin birnin don tabbatar da harkar tsaro a cikin birnin da kewaye.

Wani kamfanin kasar Amurkane ke kera baburan kuma ya shaida ma manema labarai cewa ko guda nawa Dubai din take bukata zasu samar musu dasu. Kamfanin ya bayyana cewa ko da mutum guda, ba sai hukuma ba ko kamfani ba, zai iya sayen babur din, saidai kamin a sayarwa da mutum sai an tabbatar da ya iya amfani dashi kamar yanda kafar watsa labarai ta CNN ta ruwaito.

Babban jami’in yansandan Dubai, Brigadier Khalid Nasser Alrazooqi ya bayyana cewa zasu yi amfani da baburanne dan kaiwa ga guraren dake da wahalar shiga ta kasa kuma wannan babur me tashi zai fara aiki a Dubai nan da shekarar 2020.


Photo: CNN


Photo :CNN

Ko yaushe kuke sa ran zamu iya samun irin wannan cigaba a Nigeria? Ku tura ma abokanen ku dake Facebook, whatsapp da sauransu..


Share this on:
 • 33
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  33
  Shares