buhari-zaije-England

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai tashi ranar talata ya zuwa birnin london na kasar Ingila don halartar taro na musamman da za’a gudanar kan yaki da cin hanci da rashawa.

Wannan sanarwar ta fito ne ta hannun mai magana da yawun ofishin shugaban kasa wato Mr. Femi Adesina wanda ya bayyana hakan wa manema labarai a yau asabar din nan.
Adesinan ya bayyana cewa wannan taro ne na duka kasashen duniya masu kyamar cin hanci gami da yaki dashi, inda shuwagabanni da dama zasu bada gudummawarsu akan yadda za’a kara yakar cin hanci a kasashen duniya.

Daga cikin wadanda zasu yi jawabi a gurin akwai Prime ministan Ingila wato David Cameron, da kuma shugaban babban bankin duniya Dr.Jim Yong Kim, sannan da kuma shugaba Buhari a cikin masu jawabin.

Buharin zai jawo hankalin shuwagabannin kasashen duniya wajen cire kariya ga duk wani wanda aka samu da aikata laifin cin hancin da rashawa a duk inda yake..

Sannan Buharin zai kara bayyanawa shuwagabannin yadda gwamnatinsa ke yakar cin hanci da rashewa tare da nuna bukatar su bashi tallafi wajen samun damar hukunta duk wani wanda aka samu da laifin hakan.

Daga cikin wadanda zasu raka shugaba Buhari zuwan London din akwai alkalin alkalai na kasa Alhaji Abubakar Malami, da kuma shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFFC) wato Ibrahim Magu da sauransu..

Tura wannan labarin zuwa facebook, twitter ko kuma whatsapp…