A karshen makon daya gabata ne sojojin Nigeria suka ida kakkabe dajin sambisa daga ragowar yan ta’adda na bokoharam dake cikinsa inda suka sami nasarar kashe gami da kama wasu daga cikin yan ta’addan.

Wani jami’in soja da ya kasance cikin wadanda suka gudanar da wannan operation ya bayyana cewar an jibge sojoji gami da manya-manyan makamai a dajin wanda hakan ya basu damar yakar yan bokoharam din. Ya bayyana cewa akwai daga cikin wadanda suka kama wani farar fata da ba’a bayyana ko dan wace kasa bace amma a yanzu haka yana can tsare hannun jami’an tsaro inda yake amsa tambayoyi.

Sojan ya kara da cewar a yanzu haka babu sauran yan bokoharam a cikin dajin sannan kuma sun samu nasarar tseratar da yara da mata dake tsare a hannun yan bokoharam a yayin da aka gudanar da artabun.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewar an jibge akalla dakarun soji dubu hudu da dari biyu (4200) a dajin na sambisa gabanin gudanar da samamen, inda suka shiha ta hanyoyi daban-daban da suka hada da ta Ngurosoye, Konduga/Aulari, Bama, Fulka da kuma Damboa.

Bataliya ta 152 ta shiga ta Fulka, bataliya ta 151 tabi ta gefen Banki-Darul Jamal, bataliya ta 27 tabi ta Mafa a yayinda bataliya ta 222 ta bi ta gefen Maiduguri, inda aka dauki tsawon lokaci ana fafatawa wanda daga bisani jami’an tsaron Nigeria sukayi nasara.

Muna rokon Allah ya kawo mana dawwamammen tsaman lafiya a yankinmu da kasa baki daya….