Share this on:
 • 30
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  30
  Shares


Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta bawa shugaba Buhari muhimmiyar gudunmawa wajen samun nasara a zaben shekarar 2015.

Jaruman fina-finan Hausa da mawaka sun sha halartar taron jam’iyyar APC da yakin zaben Buhari domin nuna goyon bayansu. Kazalika mawaka sun rera ma sa wakoki.

Sai dai yanzu fitowar Atiku a PDP ta janye wasu jaruman fina-finan.

Jaridar Daily trust ta tattara sunayen jaruman dake goyon bayan shugaba Buhari a zaben 2019 mai zuwa. Daga cikin jaruman Kannywood da har yanzu ke tare da Buhari akwai;

1. Adam A. Zango
2. Nura Hussain
3. Yusuf Haruna (Baban Chinedu)
4. Jamila Nagudu
5. Halima Atete
6. Rukayya Dawayya
7. Bello Muhammad Bello (BMB)
8. Dauda Kahutu Rarara (Mawaki)
9. Nazifi Asnanic (Mawaki)
10. El-Mu’az Birniwa (Mawaki)
11. Fati Nijar (Mawakiya)
12. Mawaki Aminu Ladan (ALA)
13. Hussaini Danko (Mawaki)
14. Fati Shu’uma
15. Rabi’u Rikadawa

Bayan wallafa jerin wadannan sunaye ne dai muka samu labarin cewa Jarumi Ali Nuhu Ya Nuna Goyon Bayan Shi Ga Shugaba Buhari sannan kuma muka kara samun labarin cewa Mustapha Naburaska Ya Bar Tafiyar Atiku, Ya Dawo Tafiyar Buhari.

Karanta wannan : Jerin Sunayen Yan Kannywood Dake Goyon Bayan Atiku

Ragowar jaruman fim din Hausa irinsu Rahama Sadau, Hadiza, Sadiq Sani Sadiq, Nafisa Abdullahi, da sauransu ba su bayyana dan takarar da su ke goyon baya ba.


Share this on:
 • 30
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  30
  Shares