Kotu ta yankewa dan tsohon Shugaban kasar Honduras Fobio Lobo hukuncin daurin shekaru 24 a gidan kaso.

An dai samu Fabio Lobo dan gidan tsohon shugaban kasar Honduras Porfirio Lobo da laifin safarar miyagun kwayoyi inda yake kokarin saidawa a kasar Amurka. Tuni dai aka mika shi kotu inda ta yanke masa wannan hukunci na zaman gidan kaso.

Shi dai Fabio yaso yayi amfani da damar da yake ganin yana da ita ta kasancewa dan gidan tsohon shugaban kasa wajen cin karen shi ba babbaka.

Sai dai mahaifin yaron wato shugaba Lobo ya bayyana cewar babu wani abu da zai ce don gane da wannan hukunci da aka yankewa yaron nashi fyace dai ta shi ta fishshe shi.

Ads