Gidan talabijin na arewa24 na yekuwar neman jarumai da zasu fito a cikin wani sabon tsarin shirin wasan kwaikwayo da tashar zata rika shirya wa.

Tashar Arewa24 itace tasha dake daukar nauyin gudanar da sananne kuma fitaccan wasan kwaikwayon nan da aka fi sani da dadin kowa wanda ake gudanarwa bangare-bangare.

Daga cikin guraben da ake nema akwai;

BAWA MAI KADA
Wanda za’a sa a matakin gwamna. Anaso ya kasance akalla dan shekara 55, wanda zai iya gabatar da jawabi a gaban jama’a, ya kuma kasance yana jin turanci yadda ya kamata.

HAJIYA RABI
Matar gwamna. Yar akalla shekara 45, wacce keda kwarewar magana a gaban jama’a, mai kyawu daidai gwargwado, sannan kuma ta kasance tana fahimtar yaren turanci dai dai misali.

SALMA
Yar gwamna. Kyakkyawa, yar akalla shekara 24, mai aji da kwarjini, mai kwarewa a harshen turanci da iya amfani da shi.

Sauran gurabe da ake bukatar jarumai sun hada da; SAHABI MADUGU-Dan jarida, MALAM ADAMU-Tsohon malamin makaranta, LAHAB, SAMBO, RAYYA, YOHANNA MUSA.

Daga cikin karin gurabe da ake bukata sun hada da guraben yan siyasa, yan sanda da kuma karin wasu muhimman gurabe a wasan kwaikwayon.

Domin shiga cikin manema wadannan gurabe shiga ka cike bayanan ka a wannan shafin

http://arewa24.shortstack.com/D28Lh6/l0w4K