Niger-delta-avengers

Kungiyar mayakan tsagerun Niger Delta ta fitar da sanarwar cewa kwanannan zasu harba makamai masu linzami zuwa wasu muhimman gurare a kasar nan.

Sun kuma bayyana cewa a taron da suka gudanar kwanannan sun yanke shawarar harbo tauraron dan adam din Nigeria don wai gujewa annobar da yake haifarwa akan al’umma.

Sannan sunyi kira gami da gargadin duk mutanen dake zama a guraren da zasu harba wadannan makamai masu linzami da su guji zama a wadannan gine-gine domin su a cewar su gine-ginen kawai suke so su rusa ba mutanen ba.

Sun kara da cewar zasu wahalar da gwamnati tare da kwamfanonin mai kamar yadda suka wahalar da yankunansu ta hanyar gurbata masu muhallansu da mai.

Daga cikin inda zasu harba wadannan makamai akwai: Fadar shugaban kasa(Villa) , Hukumar tsaro ta kasa , ofishin jami’an farin kaya(DSS), majalissun tarayya, NNPC, Babban bankin tarayya, kotun daukaka kara ta kasa, Ofishin Agip na Abuja, hedikwatar SHELL ta Lagos, hedikwatar Chevron ta Lagos, hedikwatar NLNG ta Abuja da Lagos, Rifanaren Kaduna da duk wasu ma’aikatu na tsaro dake Kaduna,Abuja,Lagos da Benue..

Sannan kuma sun gargadi al’umma da cewar su iya bakinsu domin duk wanda ya fadi wata mummunar magana a kansu to tabbas zai iya fuskantar fushinsu..

Me za kuce dangane da wannan ikirari? Tura wannan sako zuwa abokanenka dake facebook,twitter,whatsapp da sauransu….