Fitaccen mawakin nan na fina-finan Hausa ta kannywood Umar M Sharif ya gargadi mawallafa a yanar gizo da su daina dora masa wakoki akan shafukan su sannan kuma ya bukaci a goge wadanda aka riga aka dora.

wakokin-umar-m-sharif

Idan baku manta ba, a ranar talata 10 ga watan nan na January 2017 umar m sharif ya gargadi Abubakar Ontop akan a daina dora masa wakoki online, bayan haka kuma ya bukaci wa inda aka dora ma a cire su.

Jiya bayan sallar magriba sai na kira shi don inji ko menene dalili duba da cewar su masu dorawar a haka kamar suna masa “free promotion” ne abinda ya kamata ace sai ya biya makudan kudi kafin a sanya masa.

Amsar da ya bani itace :

Umar: Sunan da mukayi a can baya duk ta hanyar promoting dinmu online ne?

Deen: A’a amma idan ka lura da zamanin hakan a ganina kamar yana kara muku suna.

Umar: E, amma su kuma masu dorawar ai ba a banza suke dorawa ba, kaga kenan mu musha wahalar yi su kuma sai kawai su dora su ci moriyar abun. Idan ka duba naijaloaded zaka samu cewar akwai kaso da suke cire ma mawakan saboda da abunda suke samu sanadiyyar dora wakokinsu…

Deen: amma baka ganin akwai mutane da yawa dake neman wakokinku online wanda dorawar da ake ta sawwake musu wajen samun sabbin wakokinku bayanda an riga da an sayar dasu a kasuwa?

Umar: Akwai website dina da nike ginawa a yanzu haka wanda zan rika dorawa da kaina, saboda haka duk mai so sai yaje can ya dauko…

In dai takaice mu zancen a haka muka kare hirar..

Magana ta gaskiya, Duka mawakan da ake dorawa wakoki a naijaloaded basu ake biya ba face su ke zare kudin aljihunsu su biya domin a dora musu.

Abinda na fahimta daga wannan yar tattaunawar shine duk wanda yake so ya cigaba da dora wakokin M Sharif a shafinsa to dole ya ware wani kaso da zai rika bashi saboda a ganin shi kamar ana ci da guminshi a hakan..

A can baya ma dai makamanciyar hakan ta taba faruwa tsakanin Adam A Zango da Faisal M Abbas, CEO na Hausamp3, inda shima ya bukaci a dakatar da dora wakokinsa a wannan shafi na Hausamp3 inda daga bisani kuma ya hakura ya kyale.

Kalaman M Sharif din sun harzuka da yawa daga cikin mawallafan da suka kasance suna dora wakokinsa a shafukansu inda suka sha alwashin goge duka wakokinsa dake shafukansu. Ko taya kuke ganin hakan zai shafi mawakin a zamanance?