Share this on:
 • 154
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  154
  Shares

Fitacciyar jarumar nan ta Kannywood wato Rahama Sadau ta sake fitowa a cikin wani sabon film na kudancin kasar nan wato Nollywood da yanzu haka ake tsakiyar dauka.

rahama sadau

An dai ga jarumar da wata iriyar shiga wacce ta saba matuka da al’adar malam bahaushe sannan kuma uwa uba ta saba da addinin ita jarumar duk a cikin shi wannan sabon film da ake dauka wanda suka sanya wa suna “ACCIDENTAL SPY .”

Rahama Sadau a sabon film

A cikin wannan shiri anga mashahurin jarumi a harkar film na nollywood Ramsey na rike hannun jaruma Rahama Sadau wanda hakan ya kara janyo cece kuce a cikin masu kallo.

Jarumar ta nuna farin cikin ta sosai kasantuwar ta a cikin wannan sabon shiri sannan tayi farin ciki matuka akan haduwar ta da Ramsey a cikin wannan sabon film.

Ku sauke don kallon bidiyon ranar farko da aka fara haska wannan film din wanda jaruma rahama sadau ta fito a ciki.

Sauke wannan dan gajeren video daga shafin pressloaded.com ta hanyar danna
nan gurin..


Share this on:
 • 154
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  154
  Shares