Share this on:
 • 1
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  1
  Share

Rahama SadauTauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau na daya daga cikin manyan jarumai mata da suka rage da basu bayyana dan takarar da suke goyon baya ba a babban zabe me zuwa, Rahamar ta bayyana cewa, wa nene za’a yiwa yakin neman zabe a zabe me zuwa?

Rahamar ta ci gaba da magana a dandalinta na sada zumunta inda tace ita a nata tunanin abinda ya kamata a mayar da hankali shine wa za’a zaba? Maimakon wa za’a wa yakin neman zabe.

Jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu akan wannan magana tata, saidai wadda tafi kayatar da Rahamar itace wadda wani mai suna A.B Danbatta yayi.

In da yace:
“Kowanne mutum shi zai yanke hukunci kan shugaban kasar da zai zaba na gaba, babu wanda zai yanke maka wannan hukuncin sai kai da kanka. Amma ina bayar da shawara ga dukkan ‘yan Najeriya su zabi mutum na gari ko daga wacce jam’iyya yake.”

Daga nan ne Rahama Sadau ta nuna gamsuwar ta inda ta ce “Wannan ita ce amsar da nake so a ba ni.Allah ya yi maka albarka

Written by : Bashir Ahmed
Hutudole


Share this on:
 • 1
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  1
  Share