Wani matsahi ya rasa ransa a yayin gudanar da gasar neman aure ta sharo da akayi a kauyen Dirimin biri dake karamar hukumar Kafur dake Jahat Katsina.

Jaridar Punch ta ruwaito cewar an gudanar da gasar neman auren ne tsakanin mutum biyu; Yari Inusa da kuma abokin karawarsa Ahmad Saidu a yayinda shi Yari Inusa ya rasa ransa biyo bayan dukan da abokin hamayyar tashi yayi mashi a tsakiyar kai sabanin a baya kamar yadda dokar wasan ta tanada.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina DSP Gambo Isah ya tabbatarwa da jaridar Punch aukuwar wannan lamari sannan kuma ya shaida ma jaridar cewa an kama me laifin wato Ahmad Saidu.

Sharo dai wata al’ada ce ta Fulani da sukan gudanar a yayin zaba ma budurwa mijin aure domin ya kasance an samo mata jarumin namiji wanda zai iya bata kariya da kyakkyawar kulawa a koda yaushe.

Ads