Share this on:
 • 25
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  25
  Shares

Shahararren mawaki, fasihi haziki Nura Musa wanda aka fi kira da Nura M Inuwa zai fitar da sabon album dinsa na sabbin wakokin shi na bana a cikin wannan wata na Janairu.

nura m inuwa wasika 2018

M Inuwa yayi ma wannan sabon album nashi lakabi da Wasika wanda ake sa ran fitowar shi daga ranar litinin din nan mai zuwa (15th January 2018) zuwa karshen wata.

Masoya masu sauraron wakokin wannan fasihin mawaki dai sun zaku sosai da ganin cewa ya saki sabon album din wakokin sa na bana kamar yadda ya saba duk shekara.

Nura M Inuwa ya baiwa masu sauraronsa hakuri akan cewar wannan album nasa na daf da isowa gare su, saboda haka su kara hakuri.

wasika album nura m inuwa


Share this on:
 • 25
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  25
  Shares