Jama’a barkanku da warhaka, gami da fatan kun wuni cikin koshin lafiya. Dangane da tallafi na kudin mai da gwamnatin tarraya ta cire wanda hakan ya jawo cece-kuce da kuma ra’ayoyi mabambanta daga al’umar kasar nan ne yasa na yanke shawarar yin rubutu dangane da wasu daga cikin dalilan da suka sa gwamnati ta dauki wannan mataki.

an-cire-tallafi

1. Matsalar matatar mai : wannan itace babbar matsalar da ke kawo duk wannan karancin mai gami da tsadar shi da ake fuskanta. Matatun man da muke dasu a Najeriya basa iya tace kaso 30 cikin 100 na man da ake bukata a kasa, to kaga dole kenan sai an shigo da tataccen mai daga waje.

2. Bukatar Dollar: kasantuwar dole sai an shigo da mai daga waje, wanda hakan na yiwuwa ne ta hanyar amfani da dollar wacce kowa yasan yadda dollar ke tsada a kasuwar duniya yayin shigo da kaya zuwa Najeriya.

3. Matsala daga yan dakon mai: Kasantuwar sai da dollar za’ayi sayayya sai ya kasance babban bankin tarraya shine keda alhakin samar da dollar wa yan kasuwar mai. Mai makon yan dakon mai din suyi amfani da wannan daloli da aka basu sai kawai su bushe da sayar dasu a kasuwar yan canji bisa la’akari da irin kazamar ribar da zasu samu idan sukayi hakan.

4. Masu karkatar da mai: An samu bayanai da yawa kan cewa akwai masu karkatar da man da suka siyo zuwa wasu kasashen dake makwabtaka da Najeriya.

5. Wadannan matsaloli dana lissafo a sama da ma wasu matsalolin da ban samu damar zayyanowa ba sune suka janyo karanci dollar a asusun siyyaya na Nigeria wanda dole dashi ne yan kasuwarmu ke shigo da kaya. Sakamakon haka sai CBN suka dan dakatar da bayar ko kuma siyar da dollar ga su masu dakon man. Wannan mataki na CBN shine ya dan janyo tsaiko da aka samu na karancin mai.

Karin matsaloli

Na daga cikin manyan dalilan da suka sa aka cire tallafin mai;

-Rashin amfanar talaka da tallafin man keyi.

-Shigewar kudaden tallafin man zuwa aljihunan wasu yan tsirarun mutane.

-Da sauran karin wasu matsalolin.

Da yiwuwar Farashin mai ya sauko nan da wata 6

An jiyo karamin ministan mai wato Ibe Kachikwu da safiyar yau na bayyana cewa farashin mai zai rugurguzo nan da wata 6.

Dalilan da ya bada sun hada da cewar dakatar da dollar wa yan dako zaisa mutane da yawa su fita su rika saro man daga kasuwannin duniya wanda hakan zaisa kowa yayi iya bakin kokarinsa wajen ganin cewa man da ya siyo ya kare cikin sauri.

#Marubuci: DEEN DABAI
CEO arewamobile.com

menene ra’ayinku dangane da cire tallafin mai??

Ku tura wannan labari zuwa abokanenku dake facebook, twitter , whatsapp dadai sauransu.