Whatsapp ya kasance babba ko kuma daya daga cikin manyan kafofi na sadarwa ta zamani dake baka damar yin abubuwa da dama, kama daga tura sakon rubutu, sakon hoto harma da sakon murya da sauran makamantansu..

A kwanakin bayane dai kafar whatsapp ta cika shekara bakwai da ginuwa, tare murnar samun biliyoyin mutane.

Bayan wannan murnar cika shekara bakwai sai muka ji kwatsam kamfanin whatsapp ya fitar da sanarwar cewa whatsapp zai dena aiki akan wasu wayoyi masu yawa, daga ciki kuwa harda wayar blackberry.

Karin wayoyin da whatsapp zai dena aiki akansu sun hada da wayoyin Nokia da Symbian da wasu kananun wayoyin android..

Dalilin da whatsapp suka bada na daukar wannan mataki shine na cewar su wadannan wayoyin bazasu iya daukar wasu sababbin tsaruka da za’asa a cikin application din whatsapp din a nan gaba ba..

Wayon da whatsapp zai daina aiki akansu..

-BlackBerry( harda wayar BlackBerry 10)

-Nokia S40 (Java)

-Nokia Symbian S60

-Android 2.1 da kuma Android 2.2

-Windows Phone 7.1

baya ga wayoyin blackberry, masu aiki da wayoyin windows, wato windows phone suma zasu fuskanci wannan dakatarwar.

A kwanakin baya dama kamfanin blackberry ya fitar da sanarwar cewa zasu dena hado sababbin wayoyi. Hakanan ma kamfanin nokia tuntuni dama ya dena kero wayar symbian..

Idan hakan ta tabbata, to zai kasance wani babban koma baya musamman ga kamfanonin da suke kera irin wadannan wayoyin ta inda ba kowa bane zai iya hakuri ya cigaba da amfani da wayar da bata daukar whatsapp…

To ni DEENDABAI da nakasance masoyin amfani da wayar symbian ya zama dole na barta kenan sabo da rashin whatsapp ba karamin takuramin zaiyi ba..hahaha..

To masu gudu sai ince su gudu kenan…

Kuyi share na wannan labarin zuwa ga abokanku dake facebook, twitter , G+, whatsapp da sauransu..