Darasi na 1 :- Yana Da kyau Amatsayinka na musulmi Ace kasan yadda akeyin Aikin Hajji Ko umrah.

aikin hajji bana

-Ita Kalmar Hajji A larabci ma’anarta shine :- NUFI .
Amma a shari’a tana nufin bautar Allah da yin wasu ibadu na musamman da suka zo a sunnar Annabi (SAW).
-itakuma Kalmar Umrah ma’anarta shine:-ZIYARA.

Sharudan wajabcin aikin Hajji guda biyar ne, su ne:

1-Musulunci.
2-Hankali.
3-Balaga.
4-‘Yanci,Mutum ya zama da ba bawa ba
5-Iko,Lafiya, Guziri, abin hawa da Aminci.

Duk Wanda ya cika wadannan sharudai lallai ne idan lokacin Hajji ya yi ya shirya domin ya je ya sauke farali.
Slokacinda kasamu damar zuwa aikin Hajji sai ka yi kokarin mayar da duk wata Amana ga mai ita, duk wani hakki ka mayarwa mai shi, duk wani bashi ka biya, a kuma rubuta wasiyya a ajiye.

Abu na Farko Acikin Aikin Hajji shine :-

IHRAMI (Yin harama)
Daura harama shine farkon ayyukan Hajji ko Umrah wato niyyar shiga cikin ibadar Hajji ko Umrah.
Ana daura harama ne a Mikati.

MIKATI:

Shine wajen da baya halatta mai aikin Hajji ko Umrah ya ketare ba tare da ya daura Harama ba na fara aikin Hajji ko Umrah.

Mikati ya kasu zuwa kashi biyu ne :-

1. Mikati na zamani:
2. Mikati na wuri:

1. Mikatin zamani : shine lokutan fara haramar hajji yana farawa tun daga farkon watan shauwal har zuwa goman zulhajji,
Sune shawwal zulkuda da goman zulhajji ayyukan Hajji ba za su halatta ba sai acikinsu amma umrah ta halatta a watannin shekara gaba daya.

2. Mikati na wuri: sune wuraren da Akayi bayani a kansu wanda be halatta ga mai yin aikin hajji ko umrah ya tsallake su ba ba tare yayi harami ba.

Mikatai guda biyar ne (5) sune kamar haka:-

1. ZULHULAIFA

Ana kiran sa da sunan Abyar Ali mikatin mutane Madina ne da duk wanda yabiyo ta hanyar su.

2. JUHFAH

Aljuhufa mikatin mutanen Magrib da Sham da Misrah da Africa da duk wanda ya biyo ta hanyar su muma ‘yan Nigeria ana Zamu dau harami.

3. YALAMLAM

Shine mikatin mutanen Yamen da India da wanda ya biyo ta hanyar su.

4. KARNUL MANAZIL

Shine mikatin mutanen Najad da tekun fasha da duk wanda ya biyo ta hanyar su.

5. ZATU-IRK

Shine mikatin mutanen Iraki, Kurasana da Farisa da duk wanda ya biyo ta hanyar su.

Sukuma mutanen makka zasu yi niyya daga gida jensu, gidajensu shine makatinsu.
Wadannan wurare da aka ambata sune wuraren da ake daura Harama dan Aikin Hajji ko Umrah.
Wajibi ne ga duk wanda ya yi niyyar yin aikin Hajji ko Umra ya yi harama a lokacin da ya zo mikatin.

Ba lefi idan tun farko mutum bai je da niyyar aikin Hajji ba kamar wanda ya je domin kasuwanci ko karatu to shi wajabcin yin harama a mikati ba ya kansa.

Idan kuwa bayan ya wuce mikati sannan sai ya yi nufin yin aikin Hajji ko Umra, to sai ya yi harama daga inda yake, ba zai koma zuwa mikatin ba.
Amma alhazan da suka je da wuri suka fara wucewa Madina domin yin ziyara, to su sai harama daga mikatin mutanen Madina wato Zulhulaifa.

Wallahu aalam.

YADDA AKE HARAMA:-

1-WANKA:

Manzon Allah (SAW) a lokacin da ya zo mikati sai ya cire dinkakkun tufafi kuma ya yi wanka.

To wannan wanka ansone yinshi ga maza da mata, sai dai ga mai jinin al’ada ko na biki,
Wadansu malamai suna ganin wajibi ne ta yi wannan wanka.

2-SHAFA/FESA TURARE:

Domin Annabi (SAW) ya sanya turare a lokacin haramarsa,
Sai dai shi irin wannan turare a jiki ake shafa shi ba a jikin tufafin Ihrami ba.

3-CIRE DINKAKKEN TUFAFI DA SANYA ZANI DA MAYAFI:

Dalili a kan wannan shi ne Hadisin Annabi (SAW) da ya ce:-
Lallai dayanku ya yi harama cikin zani da mayafi da takalmi (silifas).

To amma fa wannan sanya zani da mayafi ga maza ne kawai.
su mata za su sa kayansu ne da suka saba sawa, in banda Nikabi da safar kafa amma za ta saka tufafinta ta lullube tun daga kanta har saman jikinta. Amma shari’a ba ta kebance wata kalar tufafi ba (Kamar fari) da za a ce lallai sai shi zata sa. Babu wata hujja a kan yin haka.

4-YIN NIYYA:

Niyya daya ce daga cikin sharuddan harama da ma dukkan sauran ayyukan ibada.

Daga nan kuma sai ya fara talbiyya ya dinga cewa:- LABBAYKAL LAHUMMA HAJJAN. Idan kuma Umrah ce sai ya ce: LABBAIKAL LAHUMMA UMRATAN.

Aikin Hajji ya kasu kashi uku, mutum ze zabi daya daga ciki wanda zai yi.

1.IFRADI.
2.QIRANI.
3.TAMATTU’I

Kafun Bayanin yadda aikin hajjin yake gabadaya.
GA bayanin Yadda Umrah take .

YADDA AKE UMRA:

Yadda ake Umra shine; da mutum ya yi Ihrami wato (Harama) kenan a Mikati sai ya yi niyya, ya fara talbiyya,

talbiyya ita ce:

لَبَّيْكَ اَللَّهُمَّ لَبَّيْكَ، لَبَّيْكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ لَبَّيْكَ، إِنَّ الْحَمْدَ وَالنِّعْمَةَ لَكَ وَالْمُلْكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ.

LABBAYKAL LAHUMMA LABBAYKA, LABBAYKA LA SHARIKA LAKA LABBAYKA, INNAL HAMDA WANNI’IMATA LAKA WAL MULKA LA SHARIKA LAKA.

YADDA AKE YIN DAWAFI:

Idan mutum ya shiga Masallacin harami cikin tsarki, sai ya dakata da yin talbiyya ya fara dawafi, mai harama zai yaye kafadarsa ta dama ya rufe ta hagu, zai fara dawafin ne ta wajen (Hajaral Aswad) idan ya sumbace shi, in kuma babu damar sumbata saboda cinkoso , sai ya shafe shi da hannu ko da wani Abu kamar sanda idan bai sami ikon shafarsa da hannu ba, kai in ma hakan bata samu ba to ya nuna shi da hannu, sai ya sumbaci hannun nasa ko na abin,
sai ya ce: “Allahu Akbar”. Sai ya fara dawafin ya sanya Ka’aba a bangarensa na hagu.
Haka zai yi a duk lokacin da ya zo wucewa ta wajen (Hajarul Aswadi) to ya yi kewaye daya kenan, sai ya sake sumbatar in kuma ba hali yayi kamar yadda ya yi da farko ya yi kabbara ya cigaba har ya yi kewaye bakwai (7), sunna ne ga namiji idan da hali ya yi sassarfa a ukun farko, a ragowar hudun kuma a tafe kawai zai yi su.

Kowanne ya fara ta wajen Hajarul Aswad kuma ya kare a nan.

Idan aka yi kokwanto yawan zagayen dawafi sai a yi gini akan mafi karanci a cigaba,
ma’ana idan kana tunanin uku ka yi ko hudu, sai ka dauka ukun ne ka cikasa ragowar.

Babu takamaiman karatu a zagayen dawafi, mutum zai iya karatun abin da ya iya na daga Alkur’ani ko addu’a ko zikiri.
Bayan ya gama Dawafin nan sau bakwai, sai kuma ya matsa bayan makamu Ibrahim ya yi sallar nafila raka’a biyu.
Raka’a ta farko Fatiha da kulya-ayyuhal kafirun, ta biyu kuma Fatiha da Kul Huwallahu Ahad.

Idan kuma babu hali saboda cikowa sai yayi nafila a duk inda ya samu iko a cikin Masallacin haramin.
Daga nan sai mai Harama ya je ya sha ruwan zam-zam.

Sai kuma yakoma ya sumbaci Hajarul Aswad, idan babu hali yayi kamar yadda ya yi a baya.

Zandakata Anan Sai Darasi Na gaba Gobe(jumma’ah) 27 GA watan shawwal Insha Allah zamucigaba.

Wassalam.

Yahaya Magaji
08031106304.

Ads