Jama’a barkanku da wannan lokaci na ranar Juma’a. A cikin wannan rubutun in sha Allahu zanyi muku bayani daya bayan daya akan yadda ake amfani da android device manager na google.

Android device manager wata manhaja ce ta yanar gizo da kamfanin google suka hada don amfanin masu rike da wayoyin android.

Android device manager na bawa masu amfani da wayar android damar yin abubuwa da dama akan wayoyin nasu ba tare da wayoyin na a hannunsu ba.

Daga cikin abubuwan da mutum zai iya yi da device manager sun hada da :

√ Gano ainihin inda wayar mutum take a yayin data fadi ko kuma ta shiga wani gurin sannan kuma a sata tayi ring da karfi koda ba SIM card din mai ita bane a ciki

√ Kulle waya da security ba tare da tana hannunka ba ta yanda babu wanda zai iya sarrafa ta se kai kadai

√ Da kuma baka damar goge dukkanin abubuwan dake cikin wayar a yayin da wayar taka ta fadi ko kuma aka sace ta.

Yadda ake amfani da android device manager

• Da farko dai dole ya kasance akwai google account(@gmail.com) akan wayar taka kafin ka iya samun damar yin amfani da android device manager domin google account din shine zai taimakawa device manager din wajen gane wayar taka yayin da kake aiwatar da bincike ta cikinsa.

Sanin duk wani mai amfani da wayar android ne cewar baza ka iya yin amfani da wayar ka dari bisa dari ba ba tare da ka sanya google account dinka a kanta ba. Misali, ba zaka iya yin amfani da playstore ba ba tare da google account dinka na kan wayarka ba.

Haka zalika ma youtube da wasu sauran abubuwan da suka shafi google sukan bukaci google account kafin su baka damar yin komai da komai akansu.

• Zaka iya dora google account dinka in ya kasance baka dora shi akan wayatka ba ta hanyar zuwa Setting > Accounts > add account > google inda za’a tambayeka Existing ko ko New.

Idan ya kasance kana da google account to sai kawai ka shiga existing sannan ka sanya gmail address da password dinka.

In kuma ya kasance baka da google account to sai ka shiga new sannan kabi matakan da zasu zayyano maka har zuwa karshe.

Da zarar ka samu nasarar dora gmail dinka akan wayar to shikenan bayanan wayarka duka zasu tafi zuwa android device manager.

Zaka iya shiga device manager ta application dinsu na android wanda zaka iya samunsa a playstore ko kuma a sawwake kayi amfani da google chrome browser sai ka shiga google.com/android/devicemanager inda za’a bukaci kayi log in da gmail address dinka.

Yanda za ka sa wayarka tayi ring

Idan wayarka ta fada wani gurin ko kuma aka dauke ta a cikin taron jama’a ko kuma dai ka rasa inda take to abinda zaka yi kawai shine sai ka sami wata wayar sannan ka shiga devicemanager sai kayi log in da gmail din dake can kan wayar taka sai ka jira ta gama loading inda zaka ga an baka zabuka guda uku sannan kuma zata nuna ainihin gari da kuma gurin da wayar taka take. Idan kana so ka sa tayi ring to sai ka sauka kasa zaka ga Ring sai kawai ka danna shi sannan kayi confirm dinsa da ok :

Yadda zaka kulle wayarka da devicemanager

Ba mamaki ka bar wayarka a gida ko a wani gurin inda baka son wani yayi amfani da wayar taka don tsoron kar a yi maka barna ko kuma a shanye maka data to sai kawai ka shiga devicemanager manager ta amfani da chrome inda zaka ga zabuka 3 ciki harda lock sai ka danna lock din inda zaka ga an kaika zuwa wani page mai dauke da akwatunan rubutu kamar yadda yake a wannan photo dake kasa:


da zarar ka gama cikewa sai ka danna lock , take wayarka zata kulle a duk inda take muddun data tana bude. Idan kuma ba bude data din take ba to zata kulle da zarar wanda ya dauki wayar ya bude data kamar yadda yake a wannan photo dake kasa

So dole se kai kadai da kasan password din zaka iya bude ta.

Yanda zaka goge komai dake kan wayar (hard reset)

Idan ya zamto cewar an sace wayarka kuma ka riga da ka fidda rai da samunta sannan kuma ya kasance akwai wasu abubuwa dlna sirri dake kan wayar da baka so wani ya gani to zaka iya ba devicemanager umarnin share kaf abinda ke kan wayar harma da na kan memory card. Yadda zaka yi shine kawai ka ziyarci devicemanager manager ta amfani da google chrome a google.com/android/devicemanager sai ka jira ta gama loading na page din sannan sai kawai ka zabi erase inda wani sabon page zai bude dauke da wani rubutu dake tambayarka Erase all data ? sai kawai ka sauka kasa ka danna Erase. Duba screenshot

Wadannan abubuwa dana zayyano a sama sune amfanin google android device manager wanda da hakan zamu iya kwatanta wayar android da wayoyin wasu kamfunan irinsu apple da sauransu.

Domin karin bayani, gyara ko kuma wata shawara za’a iya kirana ta lambata kamar haka +2348135658217 . A kira ne zaifi ba ace an bini ta whatsapp ba domin ba dole bane in kasance a whatsapp din.

Turawa abokanka…..