Wannan wani tsari ne da tuntuni wasu jama’an ke amfani da shi wajen gudanar da harkokin kiraye-kirayensu na yau da kullum a layin airtel kan farashi mai rahusa.

Da wannan tsari zaku samu damar isar da sakonninku zuwa ga masoyanku cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar kuna cikin kera a yanke muku kiran ba.

Yadda zaka ci gajiyar wannan garabasar shine ka sami layin airtel tsoho ko sabo sai ka dannan wannan code din *341 *7# sai ka kira.
Idan suka nuna maka message din cewa: “Sorry, you do not have enough balance to perfom this transaction “

to se kawai kaje ka sanya katin airtel na N200 sannan ka kara sanya code din *341*7#.

Zasu turo maka sakon cewa sun kwashe dari biyunka sannan kuma sun baka kudin da zaka yi amfani da su na tsawon sati daya

Idan kuwa suka nuna maka “Unsuccessful. This service is not allowed on your plan

To layinka bazai yi ba saboda haka sai ka nemi wani ka jaraba.

Sudai wadannan kudade da zasu baka zaka iya yin amfani dasu ne wajen kiran lambobin airtel kadai.

Domin duba ragowar kudin kiran ka sai ka danna *223# .
© arewamobile.com

Ads