Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Jama’a barkanku da wannan lokaci a cikin wata mai albarka wato watan azumiin Ramadan wanda ke kokarin yi mana bankwana, Allah ya sa mu kasance cikin yantattun bayi wadanda suka rabauta a wannan wata.

A kokarin da kamdanonin sadarwar kasar nan wajen ganin sun dada jawo kwastomomin su a jiki, yasa suke ta gasar fitowa da tsaruka masu sauki kama daga bangaren chajin kira zuwa ga bangaren garabasar data ta browsing.

A yau zamu yi bayani ne akan wani sabon tsarin garabasa da ke baiwa masu amfani da layin MTN damar more garabasar data mai yawa da kudi kalilan.

Duba da yadda sauran kamfanoni abokan kasuwanci suka yi MTN nisa wajen harkar da ta shafi ta browsing, ya sanya kamfanin fito da wannan sabon tsarin da zai baka damar more garabasar 250MB akan N100, 1GB akan N200 da kuma 4GB akan N1000.

Yadda Zaka More Wannan Garabasa

Domin more wannan garabasa sai kawai ka latsa wadannan lambobi *131*65# inda zaka ga an baka zabuka kamar haka:

 • 250MB akan N100 kwana 3
 • 1GB akan N200 kwana 7
 • 4GB akan N1,000 kwana 30

Sai kawai ka zabi wanda yayi maka a cikin wadannan zabuka dake sama.

Domin duba ragowa ko yawan data dake wayar taka sai ka latsa *131*4# ko kuma ka tura 2 zuwa 131.

Akwai korafin cewa wannan garabasa tafi yi akan tsohon layi musamman wanda aka jima ba’a sanya ma kudi ba.

Karin haske: Zaka iya amfani da wannan data akan kowacce irin manhaja dake kan waya ko ta kwamfiyuta.

Ku tura ma abokanenku dake shafukan sada zumunta na Facebook, whatsapp da sauransu.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •