Share this on:
 • 23
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  23
  Shares

Jama’a barkan ku da wannan lokaci. Shin ko kana daga cikin jerin mutanen da suka daina sanyawa layukan su na MTN kudi na tsawon lokaci sakamakon daukar musu kudi da kamfanin kanyi.?

Shin layin ka yakai kamar watanni uku ko fiye da haka ba tare da ka sanya mishi ko asi ba?

To ga wani labari mai dadi nazo maka dashi. Amma zanso ka mayar da wukar ka cikin kube don dakatar da wannan yaki da kake da MTN domin kuwa sun riga da sun mika wuya.

A kokarin da kamfanin sadarwar na MTN ke yi na ganin ya dawo da tsoffin kwastomomin shi yasa kamfanin fidda sabon tsari dake bawa tsofaffin kwastomomi da suka yi kimanin wata 3 basu sa kati ba garabasar data 2.94gb(3GB) da kuma kudin kira na tsawon mintuna 23 akan N100 kacal.

Domin cin gajiyar wannan garabasa sai kawai ka sayi katin N100 ka loda a wayarka, take zasu kwasheta su baks 3GB da kuma bonus na kimanin mintuna 23 da zaka iya kiran kowa dashi. Idan kuma katin N200 kasa to zasu baka kimanin 6GB da kuma mintuna 45 na kira.

Photo:Hausamini.com

Bonus din dai yana daukar kwanaki 15 ne sannan su kwashe in baka cinye shi ba.


Share this on:
 • 23
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  23
  Shares