Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A yau zamu yi muku bayani akan yadda zaku rinka more garabasar 500MB na data kyauta a layin MTN a kowanne wata har na tsawon wata shida.

Akwai wata sabuwar waya ta kamfanin MTN da ake siyarwa akan naira dubu takwas (N8,000) wacce idan ka saye ta ka saka layinka ciki a take zasu baka Kyautar 500MB, sannan kuma zasu cigaba da baka a duk Kowanne wata har na tsawon wata 6.

Zaka iya more wannan garabasar koda baka mallaki wannan waya ba ta hanyar amfani da fasahar canja IMEI(IMEI tweaking) dake kan wayarka zuwa IMEI din ita wannan sabuwar wayar. IMEI wasu lambobi ne guda goma sha biyar (15 digits) da kowace waya ke zuwa da su, zaka iya ganin su ta hanyar dana *#06# akan wayar ka.

A takaice dai mutum zai iya more wannan garabasar ba tare da ya kasance ya mallaki wannan wayar ba, illa iyaka dai ya kasance ya samu IMEI na wayar da ake bukata sai ya sanya a tashi wayar.

Har wa yau kuma, zaku iya samun kyautar 500MB ta hanyar dauko MyMTN app akan wayar ku, wanda zaku iya samunsa a Google playstore.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •