Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Jama’a barkanku da wannan lokaci. A yau muna dauke da bayani akan yadda zaku more garabasar data ta browsing a kan kowanne layi( MTN, Airtel, Glo da kuma Etisalat).

Abubuwan da ake bukata

 • Wayar Android
 • Layin waya(ko wane irine)
 • Manhajar Flaim (zan baku link da zaku dauko ta a kasa).

Ba tare da bata lokaci ba, ka dauko wannan manhaja ta Flaim akan wayar android dinka (download link yana kasa)

Daga nan sai ka bude Manhajar za kaga gurin da aka bukaci mutum ya sanya lambar wayar shi, sai ka saka lambar taka.

Zasu turo maka verification message mai dauke da lambobi guda 6 wadanda zaka sanya a gurbin verification din.

Da zarar ka gama verification zaka ji anyo maka sakon data (750mb) ko kuma kati na kira (N500) a wayarka( sai ka duba yawan data dake kan layin zaka gani).

Daga nan zaka ga sun kai ka wajen da zaka sanya username da kuma status update naka, daga nan sai kuma kaga an kaika wajen sanya DP(Display Picture) ko kuma profile picture, shikenan ka gama sai dai in kana bukatar kari to zaka gayyato abokanenka ta hanyar “invite” button dake cikin manhajar.

Karin bayani: ba zaka kulle wannan manhaja ta Flaim ba a yayin da kake jiran zuwan verification code din, sannan ka sani code din zai iya daukar kamar mintuna goma (10 minutes) kafin ya shigo, saboda haka sai mutum ya jira har sai sakon ya shigo.

Zaka sami karin data ko kudin kira a duk lokacin da ka gayyato abokanka sukayi register.

Domin sauke wannan manhaja ta Flaim sai ka latsa nan gurin.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •