Barkan ku da wannan lokaci daukacin maziyarta shafin arewamobile. Shafi da kan kawo maku bayanai a bangarori dabam-daban na abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum.

A yau zan yi muku dan takaitaccen bayan akan yadda zaku sauke hoto ko bidiyo daga status na whatsapp da mutane ke dorawa. Da wannan bayani da zan yi muku zaku huce takaicin tambayar wani akan ya turo muku da video ko hoto daya dora a status dinsa.

A farkon shekarar nan da muke ciki ne dai shahararren kamfanin sadarwar nan ta zamani wato whatsapp ya fito da wasu sabbin zubi da tsaruka a cikin sabuwar manhajar da suka fitar, wanda sanadiyyar hakan ne manhajar ta whatsapp ta daina aiki akan wasu wayoyin masu kananun zubi.

Yadda ake ajiye status na whatsapp

Hanyoyin da zamu yi amfani dasu guda biyu ne;

1. Ta file manager

2. Ta amfani da application na daukowar (third-party apps)

Ta File manager

Da farko dai ka tafi ta file manager din wayarka, sai ka bude menu option ka zabi “show hidden items.

Bayan nan sai ka nemi folder ta whatsapp > Media > zaka ga .statuses sai ka shiga. A nan ciki zaka ga hotuna da bidiyoyi da mutane ke dorawa akan status na whatsapp dinsu.

kada ka mance da cewar: status din yana goge kansa bayan awa ashirin da hudu(24), a sabili da haka sai kayi kokarin kwafe shi zuwa wata folder akan Memory card ko kan wayarka. arewamobile.com

Ta amfani da third-party applications

Manhajar da zaka yi amfani da ita itace whatsapp status saver , wacce zaka iya samu a nan gurin ko kuma playstore.

Bayan nan sai kayi installing na manhajar sannan ka bata damar iko akan wayar taka (grant permission).

Daga nan zata rika ajiye maka duk wasu hotuna da bidiyoyi da mutane suke dorawa akan status dinsu.

Zaku iya kallon wannan dan takaitaccen video tutorial da nayi don karin bayani.

Daga yanzu ka huta da tambayar abokin ka akan ya turo maka video ko hoto daya dora a kan status dinsa.

Marubuci: Deendabai
Ceo, arewamobile.com.

Ads